Alkalan wasa sun yi barazanar kauracewa gasar premier a Najeriya

Super Eagles
Image caption Tawagar 'yan kwallon Najeriya

Alkalan wasan kwallon kafa a Najeriya sun ce ba zai yiwa ba a fara gasar premier ta kasar a ranar biyu ga watan Oktoba har sai an biyasu bashin da suke bi.

Shugaban kungiyar alkalan wasa a Najeriya Ahmed Maude ya jaddada cewar zasu kauracewa gasar idan ba a sasanta ba.

Maude ya bayyana cewar suna bin hukumar dake kula da gasar premier ta Najeriya NPL bashin dala dubu saba'in.

"mun shirya tsaf a fara gasar amma dai sai an biyamu kudadenmu sannan mu shiga fili",in ji Maude.

A ranar Asabar ne sakataren riko na NPL, Tunji Babalola ya sanarda cewa za a fara gasar a mako mai zuwa inda Kaduna United za ta kece raini da Kano Pillars.