Zan koma Manchester United idan ta nemi ni-Sneijder

 Sneijder
Image caption Wesley Sneijder ya ciwa Holland kwallaye a Afrika ta Kudu

Dan kwallon Inter Milan Wesley Sneijder yace idan har Manchester United ta nuna sha'awa akanshi, tabbas zai taka mata leda.

Dan kasar Holland din ya jaddada biyayyarsa ga Inter Milan duk da cewar sun kasa cimma daidaito wajen sabunta yarjejeniya tsakaninsu.

Amma dai ya bayyana cewar ba zai iya cewa United a'a ba, idan har tayi zawarcinshi.

"Duk wanda ya tambaye ni zan takawa Manchester United leda, ba zan iya cewa a'a ba", Sneijder ya shaidawa jaridar Daily Star Sunday.

Sneijder ya ce United na daga cikin manyan kungiyoyi a duniya, sannan kuma gasar Premier tana burgeshi.