UEFA:Drogba zai jagoranci Chelsea tsakaninta da Marseille

Drogba
Image caption Didier Drogba zai kara da tsohuwar kungiyarshi Marseille

Dan kwallon Chelsea Didier Drogba zai komo daga dakatarwar da akayi mashi kuma ana saran zai jagoranci kungiyar a karawarta da Marseille a Stamford Bridge na gasar zakarun Turai.

Dan wasan Ivory Coast din mai shekaru 32 bai taka leda ba a wasanda Chelsea ta lallasa Zilina daci hudu da daya.

Sai Frank Lampard da Yossi Benayoun duk ba zasu buga ba amma dai watakila Ashley Cole ya taka leda.

A bangaren Marseille dan kwallonta na baya Souleymane Diawara ya murmure daga raunin da yake fama dashi.

Sauran karawar da za ayi a ranar Litinin:

*Spartak Moscow v MSK Zilina *Ajax v AC Milan *Auxerre v Real Madrid *Basle v Bayern Munich *Braga v Shakhtar Donetsk *Partizan Belgrade v Arsenal *Roma v CFR 1907 Cluj-Napoca