AYC:Ghana ta dauki matakin kare kofinta

Ghana
Image caption Black Satellites na Ghana bayan sun lashe gasa a Masar

Zakaran gasar cin kofin duniya ta 'yan kasada shekaru 20 wato Ghana ta dauki gaggarumin matakin kare kofinta na Afrika bayan ta doke Benin daci biyu da nema a Cotonou .

Kungiyar Black Satellites ta kasance ta farko a Afrika data lashe gasar cin kofin duniya ta 'yan kasada shekaru 20 a bara inda Enoch Ebo Andoh da Richmond Boakye Yiadom suka ci kwallon.

A halin yanzu dai kasashe 14 ne ke buga wasannin share fage don neman cancantar buga gasar a Libya a badi.

Za ayi bugu na biyu na wasannin share fagen a karshen makon 22-24 na Oktoba.

Kamaru wacce ta sha kashi a wajen Ghana a wasan karshe a bara, a wannan karon Kamarun ta doke Congo daci daya me ban haushi a Brazzaville.

Senegal ta samu galaba akan Masar daci daya da nema a dakar, Lesotho ta casa Kenya a Nairobi daci daya, Flying Eagles na Najeriya ta doke Mauritius daci biyu da nema sai kuma Gambia wacce ta casa Ivory Coast daci daya.