Ancelotti:Har yanzu Lampard bai gama mumurewa ba

Lampard
Image caption Frank Lampard na murnar zira kwallo

Frank Lampard ba zai taka leda ba a wasu muhimman wasannin Chelsea da Ingila a yayinda yake cigaba da murmure sakamakon fidar kaban ciki da aka yi mashi.

Dan shekaru 32, Lampard ya shafe wata guda baya kwallo, sannan kuma kocinsa Carlo Ancelotti ya tabbatar cewa zai cigaba da jinya daga nan har zuwa makwanni biyu masu zuwa.

A wannan lokacin zai rasa wasansu da Marseille dana Arsenal da kuma na Ingila tsakaninta da Montenegro.

Lampard ya komo horo bayan an yimashi fidar a 31 ga watan Agusta amma dai yana jin zafi a cikinshi.

Rabonshi daya bugawa Chelsea tun a ranar 28 ga watan Agusta inda suka doke Stoke City daci biyu da nema.