Kungiyar Sevilla ta kori kocinta Antonio Álvarez

Gregorio Manzano
Image caption Sabon Kocin Sevilla Gregorio Manzano

Kungiyar Sevilla ta Spain ta kori Antonio Álvarez a matsayin mai horadda 'yan kwallonta saboda kasa taka rawar gani a kakar wasa ta bana.

Sevilla ta kori Álvarez bayan kungiyar tasha kashi a wajen Hércules daci biyu da nema.

A yanzu haka an nada Gregorio Manzano a wanda zai maye gurbinshi.

Álvarez ya shafe watanni shida ne kadai a kungiyar sannan kuma ya kasa tsallakewa zuwa gasar zakarun Turai bayan da kungiyar Sporting Braga ta Portugal.