Hukumar FA na tuhumar kocin Blackpool Holloway

Holloway
Image caption Ian Holloway rike da kofin da ya kaisu gasar Premier

Hukumar dake kula kwallon Ingila FA na tuhumar kocin Blackpool Ian Holloway saboda amfani da mugayen kalamai akan alkalin wasa.

A lokacin dai Blackpool ta sha kashi a gidanta a wajen Blackburn inda aka zira kwallo daya a cikin karin lokaci bayan cikar minti casa'in.

Holloway yace:"Alkalin wasa Mike Dean bai dauki hukunci yadda ya dace ba".

A karkashin sabuwar dokar FA, Holloway nada kwanaki uku ya maida martani.