Manchester na bukatar sabon tarihi a Spain

Fergie
Image caption Sir Alex Ferguson na tunanin rashi Rooney

Manchester United na kokarin kawo karshen mummunar rawa a gasar kwallon Turai idan ta je Spain a yayinda zata kara da Valencia a gasar zakarun Turai a ranar Laraba.

United ta samu nasara ne a wasa daya tal cikin guda 18 data fafata da kungiyoyi a Spain, nasarar United din shine tsakaninta da Deportivo La Coruna a gasar da aka buga a shekara ta 2002.

Kocin United Sir Alex Ferguson a wasansu na farko a kakar bana a gasar dai, sun tashi babu ci tsakaninsu da Rangers.

A bangaren Valencia kuwa ta casa Bursaspor ne daci hudu da nema.

Ryan Giggs da Wayne Rooney duk ba zasu taka leda a wasan saboda rauni a yayinda Micheal Owen da Dimitar Berbatov zasu jagoranci gaba.