FIFA za ta biya fansa ga golan Togo Obilale

Obilale
Image caption Golan Togo Kodjovi Obilale

Golan Togo Kodjovi Obilale wanda aka harba sau biyu a bayanshi a Angola lokacin gasar cin kofin kasashen Afrika yace FIFA ta yi mashi alkawarin dala dubu 25 don ya cigaba da neman magani.

A watan daya wuce ne maaikatar wasanni ta kasar Togo itama ta bashi dala dubu 70 don ya cigaba da daukar dawainiyar kanshi.

Obilale mai shekaru 25 yanzu wata takwas kenan ya kasa tafiya sakamakon harbin, inda aka kashe mutane biyu cikin tawagar Togon a Angolar.

A cewar golan, abinda ya faru dashi da ace irinsu Drogba ne ya faru dasu, da ba za a kwaleshi ba.