Bana shirin kara zuwa Turai don taka leda-Beckham

Beckham da Capello
Image caption David Beckham lokacin yana dasawa da Fabio Capello

David Beckham ya ce baya shirin kara zuwa Turai don kasancewa dan kwallon aro duk da cewar yanada muradin sake bugawa Ingila kwallo.

Beckham ya shafe lokaci a matsayin aro a AC Milan cikin shekaru biyun da suka wuce idan ana hutu a Amurka don ya kasance garau a yin kurinshi na bugawa kasarshi kwallo.

AC Milan ta riga ta bayyana cewar ba zata kara siyen dan shekaru 35 din ba a karo na uku bayan da rauni ya hanashi zuwa gasar cin kofin duniya.

Beckham ya ce yana saran rawar da yake takawa a gasar kwallon Amurka tare da LA Galaxy zata sa kocin Ingila Fabio Capello ya canza ra'ayinshi don sake kiranshi a tawagar kasar.

Kawo yanzu dai Beckham ya takawa Ingila leda a wasanni 115.