FIFA ta bullo da sabon tsarin wajen musayar 'yan kwallo

Blatter
Image caption Sepp Blatter ya sha alwashin tsabtace musayar 'yan kwallo

Daga ranar daya ga watan Oktoba, hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce dole ne abi sabon tsarin amfani da fasaha wajen musayar 'yan kwallo a duniya.

Sabon tsarin mai suna TMS za ayi amfani da intanet ne don tabbatar da cewar anyi musayar 'yan kwallon cikin sauki ba tare da kumbiya kumbiya ba.

A fara amfani da tsarin ne a watan Fabarairu na shekara ta 2008 a matsayin gwaji a kasashe 18 inda kungiyoyi 3,633 suka shiga ciki.

Shugaban FIFA Sepp Blatter ya ce "wani sabon mataki ne a tarihi kuma muna saran zai taka muhimmin mataki wajen musayar 'yan kwallo".

Mahimmancin wannan sabon tsarin dai zai kara kawo gaskiya wajen musayar 'yan kwallo kuma ya taimaka wajen yaki da halarta kudaden haramun da kumbiya kumbiya wajen harkar sayen 'yan kwallo.