Alberto Contador ya musanta zargin shan miyagun kwayoyi

Alberto Contador
Image caption Alberto Contador

Zakaran gasar tseren keke ta Tour de France Alberto Contador ya musanta zargin shan kwayoyin da aka haramta wa 'yan wasa inda ya yi ikirarin cewa gurbataccen abinci ya ci.

Matukin keken ya lashe gasar ce har sau uku a baya kuma an zarge shi ne da shan kwayoyin da aka haramta, wanda kuma za su taimaka mishi wajen tsere.

Contador mai shekarun haihuwa 27 ya ce yaci wani nama ne da aka kawo mishi daga kasar Spain wanda ta gurbace a lokacin gasar ta bana, wanda kuma ya ke ganin cewa shiya ya nuna a gwajin da aka yi mishi.