Barcelona ta tashi kunen doki tsakaninta da Mallorca

Messi
Image caption Gwarzon dan kwallon duniya Lionel Messi

Barcelona karkashin jagorancin Pep Guardiola ta tashi daya da daya tsakaninta da Real Mallorca a filin wasa na Nou camp a ranar Lahadi.

Wannan sakamakon ya maida Barca din ta hutu akan teburin gasar La Liga

Sakamakon sauran karawar da akayi:

*Real Zaragoza 2 - 2 Sporting Gijón *Real Sociedad 1 - 0 Espanyol *Valencia 2 - 1 Athletic Bilbao *Sevilla 3 - 1 Atlético Madrid *Getafe 3 - 0 Hércules *Villarreal 2 - 0 Racing Santander *Almería 1 - 1 Málaga *Osasuna 1 - 1 Levante