Mancini:Adebayor na bukatar ya fara cin kwallaye

Adebayor
Image caption Dan kwallon Togo Emmanuel Adebayor

Kocin Manchester City Roberto Mancini yace dole sai Emmanuel Adebayor ya koma cin kwallaye idan har yana son ya cigaba tare dasu.

Dan kwallon kasar Togo, a kakar wasa ta bana ba a fara wasa dashi ba a City kuma ya kasa cin kwallo a wasanni shidan daya buga.

Mancini yace"muna son ya koma fasa raga, abinda muke aiki akanshi kenan".

Adebayor a halin yanzu yana cikin damuwa saboda baya bugawa sosai sannan zuwan Mario Balotelli yasa ana tunanin za a sayarda shi.