An baiwa Odemwingie kyautar dan kwallon premier

Odemwingie
Image caption Dan kwallon Super Eagles Osaze Odemwingie

An nada kocin West Brom Roberto Di Matteo a matsayin kocin daya fi kowanne nuna kwazo a gasar Premier ta Ingila na watan Satumba.

Kungiyar Baggies ta samu maki bakwai cikin wasanni uku a watan daya wuce, hadda nasarar daya samu akan Manchester City da Arsenal,kuma sune na shida akan tebur.

Shi kuma Peter Odemwingie shine dan kwallon daya fi nuna bajinta a watan daya wuce din.

Odemwingie dan kwallon Najeriya ya koma Lokomotiv Moscow a watan Agusta ya ci kwallaye uku cikin wasanni biyar.