Ba zan kara komawa gasar premier ta Ingila ba-Pique

Pique
Image caption Tsohon dan kwallon Manchester United Gerard Pique

Dan kwallon bayan Barcelona Gerard Pique ya ce ba zai kara komawa taka leda a gasar premier ta Ingila ba,abinda ya kawo karshen jita jitar zuwa Manchester City.

Dan shekaru ashirin da uku a baya bayannan ne aka alakantashi akan zuwa City akan pan miliyan casa'in.

Tsohon dan kwallon Manchester United yace: "Nima naji jita jitar, amma ina na daram a Barcelona".

Rahotanni sun nuna cewar City na son biyan pan miliyan takwas a kowacce shekara har na tsawon shekaru biyar,kuma ana ganin cewar City din na son amfani da Yaya Toure don ya janyo hankalin Pique.