'Yan kallo 2000 na jiran Fifa ta mayar musu da kudin tikiti

'Yar kallo da tikiti
Image caption 'Yar kallo da tikiti lokacin wasan karshe na gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu

Fiye da mutane dubu biyu ne ke jiran hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta mayar musu da kudin tikitin shiga filayen wasa na gasar cin kofin duniya da aka kamalla a Afrika ta Kudu.

Mutannen dai sun mayarwa da Fifa tikitinsu don a siyar a mayar musu da kudadensu ta hanyar cinikayya a intanet.

Masu shirya gasar dai sun dauki alkawarin maidoda kudaden cikin makwanni hudu da kamalla gasar wato daga ranar 11 ga watan Yuli.

Sai dai kawo yanzu Fifa ta kasa mawarya da 'yan kallo kusan 21,500 kudinsu.

An fuskanci matsaloli da farko wajen siyarda tikitin shiga filayen wasa a gasar cin kofin duniya ta hanyar intanet inda 'yan Afrika ta Kudu suka kasa cin moriyar tsarin.

Amma bayan da aka fara sayarda tikitin akan kanta, an siyarda akalla tikiti dubu dari daya a kwanaki biyu na farko.