Fifa ta dakatar da Najeriya a kwallon kafa

Super Eagles
Image caption Tawagar 'yan kwallon Super Eagles

Hukumar dake kula da kwallon kafa a duniya Fifa ta dakatar Najeriya daga shiga harkokin kwallon kafa saboda gwamnati na tsoma baki akan lamarin.

Dokokin Fifa sun haramtawa gwamnati saka hannu wajen gudanar da kwallo a kowacce kasa.

Fifa ta dauki hukuncin ne a ranar Litinin bayan da aka gabatar da mafi yawan wakilan NFF gaban kuliya akan zabensu da akayi.

Fifa tace"taron gaggawa da muka gudanar a yau, shine dakatar da NFF ba tare da bata lokaci ba".

Hukuncin dakatar da Najeriyar da harkar kwallo a duniya ya janyo tababa akan wasan da kasar zata buga tsakaninta da Guinea a birnin Conakry na neman cancantar buga gasar cin kofin kasashen Afrika.