Bayani kan teburin gasar Commonwealth

Baicin bayyana sakamakon wasannin da ake gudanarwa a yanzu, wanda ya kunshi zinare/azurfa/tagulla da kuma jimillar lambobin da aka ci, wannan jadawalin yana dauke da wasu hanyoyin na daban da za a iya fassara matsayin kowacce kasa. Idan ka latsa wani Tab, wannan zai sauya, ya kuma musanya rukuni na karshe kamar yadda aka yi bayani a kasa.

  • Karkashin tab din gabadaya, jadawalin zai kunshi adadin tagulla, azurfa da zinare da kowacce kasa ta lashe a gasar Commonwealth ta shekarar 2010. Rukunin shekarar 2006 na nuna jimillar lambobi da kasa ta lashe a gasar da aka gudanar a Melbourne a shekarar 2006.
  • Karkashin tab yawan al'umma, rukunin 'yawan lambobi ga kowanne dan kasa' na nuni da yawan al'ummar kowacce kasa idan aka kwatanta da yawan lambobin da kasar ta samu.
  • Karkashin tab din GDP/Karfin tattalin arzikin kowacce kasa, rukunin karfin tattalin arzikin kowacce kasa na nuni da kwatankwacin yawan tattalin arzikin kowacce kasa idan aka raba da lambobin da kasar ta samu.