Yobo ya bukaci Najeriya ta sasanta da Fifa

Yobo
Image caption Kaptin din Super Eagles Joseph Yobo

Kaptin din Super Eagles na Najeriya Joseph Yobo ya yi kira ga hukumomin dake tafiyar da wasanni a kasar suyi kokarin ganin Fifa ta dage dakatarwar data yiwa Najeriya.

A ranar Litinin ne Fifa ta dakatar da Najeriya daga shiga kwallo a duniya saboda a cewarta gwamnati na katsalanda a harkar wasanni.

Wannan dakatarwar ya kawo tababa akan wasan da Najeriya zata kara da Guinea abinda yasa Yobo ya kosa a sansanta.

Yobo yace"wannan abun babu dadi ga magoya baya da 'yan kwallon da kuma kasar baki daya".

Dan kwallon dake taka leda a Fenerbahce yace yunkurin 'yan kwallo na maidoda martabar kwallo a kasar zaici karo da cikas idan har ba a magance matsalar NFF din ba.

Hukumar ta FIFA ta ce ta dauki wannan matakin ne saboda matakin kotu da gwamnatin Najeriya ta dauka akan 'yan kwamitin hukumar kwallon kafar kasar wato NFF.

Har wa yau matakin ministan wasannin kasar na fara gasar league league ba tare da wasu kungiyon kwallon kafar kasar sun koma taka leda a karamar gasar kasar ba, bai yiwa Fifa dadi ba.