Micheal Ballack sai a badi zai koma taka leda

Ballack
Image caption Kaptin din Jamus Micheal Ballack

Dan kwallon Bayer Leverkusen Michael Ballack sai a watan Junairun badi ne zai koma taka leda.

Dan kwallon ya jimu ne a wasan Leverkusen da Hannover a ranar 11 ga watan Satumba kuma tun daga lokacin da sanduna yake tafiya.

An yiwa Ballack gwaji a ranar Talata don ganin yadda yake murmurewa, amma sai aga cewar tsananin ciwon ya wuce yadda aka yi hasashe.

Kocin Leverkusen Jupp Heynckes ya bayyana cewar "wannan lamarin nada takaici, amma ina saran idan Micheal Ballack ya dawo badi zai kara karfinmu".

Dan shekaru talatin da hudu, Ballack ya bar Chelsea ya koma Leverkusen amma ya kasa tabuka abin azo a gani saboda rauni.