Yossi Benayoun zai dade yana jinya

Benayoun
Image caption Yossi Benayoun tun a watan daya wuce rabonshi da taka leda

Dan kwallon Chelsea Yossi Benayoun zai shafe watanni yana jinya saboda rauni a kafarshi.

Hukumar kwallon kasar Isra'ila ta ce kaptin din 'yan kwallon ta mai shekaru talatin ya raunata a lokacin data gayyaceshi don buga wasanni biyu tsakaninta da Croatia da kuma Girka na neman cancantar buga gasar kwallon kasashen Turai.

Adreshin yanar gizon kwallon Isra'ila ya ce za ayi gwaje gwaje kafin a san tsanannin ciwon da Benayoun yake fama dashi.

Benayoun yaci kwallaye uku a wasansu da Malta sannan kuma ya buga wasansu da suka tashi babu ci tsakaninsu da Georgia.

Amma dai bai kara taka leda ba tun lokacin da Chelsea tasha kashi a gidanta a wajen Newcastle a wasan kofin Carling a ranar ashirin da biyu da watan Satumba.