Wani sabon kampani zai sayi kungiyar Liverpool

Hicks da Gillet
Image caption Masu Liverpool Tom Hicks da George Gillet

Za a sayarda Liverpool ga masu kungiyar kwallon Boston Red Sox na Amurka.

Sai dai batun sayen kungiyar wadda kampanin New England Sports Ventures zai yi na bukatar warware batutuwa tare da masu kungiyar na yanzu wato Tom Hicks da George Gillett.

Kungiyar ta Liverpool wacce ke taka leda a gasar premier League kawo yanzu taki cewa komai akan batun.

Tunda farko Hicks da Gillett sunyi kokarin korar manajan darektan kungiyar Christian Purslow da kuma darektan kasuwanci Ian Ayre a yinkurin cigaba da rike madafan ikon kungiyar.