Chung zai kalubalanci Blatter a takarar shugabancin Fifa

Chung da Blatter
Image caption Chung Mong-joon da Sepp Blatter a taron Fifa

Mataimakin shugaban Fifa Chung Mong-joon daga Koriya ta Kudu ya ce zai yi takara da Sepp Blatter a zaben shugabancin kungiyar a watan Mayun badi.

Chung me shakaru 58 ya bayyana a jawabinshi wajen taron kolin shugabannin kwallon kafa a London cewar "yayi wuri ace babu hammaya a takarar Mayu mai zuwa".

Da aka tambayeshi ko zai tsaya takara, sai yace "nayi tunanin haka, kuma zan sake nazari akai".

Chung na daga cikin iyalan masu kamfanin Hyundai a Koriya ta Kudu kuma yana daya daga cikin mataimakan shugaban Fifa guda takwas mai fada aji.

Mohamed Bin Hammam na Qatar, shugaban hukumar kwallon nahiyar Asiya-AFC ya riga ya bayyana cewar ba zaiyyi takara da Blatter ba a 2011.

Blatter dan kasar Switzerland mai shekaru 74 ya dare shugabancin Fifa ne a shekarar 1998 bayan ya doke shugaban Uefa na wancan lokacin Lennart Johansson.

Blatter ya sake cin zabe a 2002 bayan ya doke Issa Hayatou shugaban Caf,sannan kuma aka sake zabenshi babu hamayya a 2007.