Tom Hicks zai kalubalanci sayarda Liverpool gaban kuliya

Tom Hicks
Image caption Tom Hick Jnr dan wanda zai kai kara kotu

Tom Hicks ya sha alwashin kai kara gaban babbar kotu don nuna kin amincewa da batun sayarda Liverpool akan pan miliyan dari uku.

Kwamitin gudanarwa na Liverpool ya amince da yarjejeniya da kampanin New England Sports Ventures amma dai Hicks da Gillett wadanda suke mallakar kungiyar sunce sun kori darektoci biyu kafin ayi cinikin.

Sai dai shugaban kungiyar Martin Broughton ya bayyana cewar Amurkawan ba suda ikon canza wakilan kwamitin gudanarwan.

A halin yanzu dai bangarorin biyu sun shirya zuwan kotu don warware matsalar.