Wesley Sneijder zai sabunta kwangilarshi a Inter Milan

Sneijder
Image caption Wesley Sneijder ya haskaka tare da Holland a Afrika ta Kudu

Rahotanni na nuna cewar dan kwallon Holland Wesley Sneijder ya koma tattaunawa da kungiyar Inter Milan akan batun sabunta yarjejeniyarshi zuwa shekara ta 2015.

Rohatanni dai sun bayyana cewar an samu rashin jituwa akan batun sabon kwangilar tsakanin Sneijder da mahukunta a Inter saboda batun karin kudi, amma dai an gano cewar a halin yanzu sun koma kan teburin sasantawa akan batun kwangilar.

Kuma Sneijder ya tabbatar da cewar suna kan yarjejeniyar.

Sneijder ya shaidawa wata mujalla cewar "wannan ce kungiya ta, daga nan zuwa makwanni biyu masu zuwa zamu sabunta yarjejeniyar".

Anasaran zai sanya hannu a kwangila har zuwa shekara ta 2015 kuma za a kara kudin alawus din daga Euro miliyan hudu a shekara zuwa Euro miliyan shida a kowacce shekara.