Ingila ta kira Stewart Downing don maye gurbin Lennon

Dowing
Image caption Dan kwallon Aston Villa Stewart Downing

An kira Stewart Downing a tawagar kwallon Ingila don maye gurbin Aaron Lennon wanda ke fama da ciwon baya cikin wadanda zasu buga wasan share fage tsakaninsu Montenegro na gasar cin kofin kasashen Turai .

Dan kwallon Tottenham Lennon ya kasance dan kwallo na biyu cikin kwanaki biyu daya janye daga tawagar Ingila bayan Phil Jagielka ya samu rauni a kafadarshi.

Downing me shekaru 26 wanda ke taka leda a Aston Villa tun watan Maris din 2009 rabon daya bugawa Ingila kwallo.

Haka zalika Gary Cahill na Bolton Wanderers ne zai maye gurbin Jagielka.