CAN 2012:Nijer ta yiwa Masar ba zata a Yamai

Masar
Image caption Tawagar 'yan kwallon Masar na murnar lashe gasar Afrika a 2008

Zakaran kwallon Afrika Masar ta sha kashi a wajen Nijer daci daya me ban haushi a wasan da aka buga ranar Lahadi a birnin Niamey.

Tawagar Menas din ta samu galaba dinne a wasan rukunin G na gasar cin kofin kasashen Afrika da za a buga a 2012.

Ouwa Moussa Maazou wanda ke taka leda a Faransa shine ya zira kwallon bayan an samu kuskure a bayan Masar.

Tawagar Pharaohs wacce take ta tara a duniya ta kasa doke Nijer wacce Fifa tace itace ta 154 a duniya.

A halin yanzu dai bayan karawa biyua rukunin G, Nijer nada maki daya a yayinda Masar keda maki guda.

Sai a watan Maris na badi Nijer zata hadu da Sierra Leone a wasanta na gaba a yayinda Masar zata garzaya Johannesburg don karawa da Afrika ta Kudu.