Babu tantama zamu sayarda Liverpool- Purslow

Liverpool
Image caption Magoya bayan Liverpool na cikin damuwa akan cinikin

Shugaban Liverpool Christian Purslow yace baida haufin cewar kamfanin New England Sports Ventures zai mallaki kungiyar nan bada jimawa ba.

Idan har sabon kamfanin ya karbe madafan iko a kungiyar, za a share bashin pan miliyan dari uku da ake bin kungiyar, abinda kuma zai kawo karshen durkushewar babban kamfanin Kop Holdings wanda a yanzu shike da Liverpool.

Purslow ya shaidawa: "babu abinda ya shiga gabanmu tabbas zamu kamalla yarjejeniyar".

Tom Hicks da George Gillett wadanda keda kungiyar a yanzu sunki amincewa da cinikin kuma zasu kalubalanta a babbar kotu saboda suna tunanin tayin da akayi baikai rabin kudin darajar kungiyar.

Bankin Royal na Scotland na bin Amurkawan pan miliyan 280 wadanda dole ne su biya daga nan zuwa 15 ga watan Oktoba.