Rafael Nadal ya lashe gasar Japan Open

Nadal
Image caption Rafael Nadal ya lashe kofina 43 a duniya

Zakaran wasan Tennis a duniya Rafael Nadal ya doke Gael Monfils da seti biyu a jere inda ya lashe gasar Japan Open a Tokyo.

Dan Spain din me shekaru 24 wannan nasarar ta kasance gasa ta bakwai daya lashe a kakar wasa ta bana.

Nadal yace"ina son kamalla bana ta hanya mai dadi tare da lashe gasa dayawa".

Ya kara da cewar "zan so in cigaba da gwadawa daga nan har zuwa Shanghai kai har karshen kakar wasa wajen doke abokan karawa na".

Cikin minti saba'in da bakwai Nadal ya doke Monfils a lokacin karawar, kuma wannan kofin ya kasance na 43 da dan Spain din ya daga cikin harda gasar kofin Wimbledon dana US.