Ferdinand ya kara dawowa a matsayin kaptin din Ingila

Ferdinand da Rooney
Image caption 'Yan Manchester United da Ingila Rio Ferdinand da Wayne Rooney

An tabbatar da Rio Ferdinand a matsayin kaptin din tawagar Ingila a wasan share fage na gasar kasashen Turai na 2012 da zasu kara da Montenegro a filin wasa na Wembley.

Dan kwallon bayan Manchester United ya sake karbe kambumshi ne daga hannun kaptin din Liverpool Steven Gerrard wanda ya daana lokacin Ferdinand na jinya.

Baya ga haka dan kwallon Sunderland Darren Bent ba zai buga wasan ba saboda raunin daya samu lokacin horo a ranar Litinnin a don haka watakila a fara wasan da Peter Crouch.

John Terry ma ba zai buga wasan ba saboda ciwon baya sannan kuma dan kwallon Everton Phil Jagielka ya kamu da rauni a kafadarshi abinda ya janyo Ferdinand zai buga baya tare da Joleon Lescott na Manchester City.