Dan Arsenal Bacary Sagna ya samu rauni

Sagna
Image caption Dan Faransa Bacary Sagna

Arsenal zata taka leda ba tare da Bacary Sagna a wasanninta biyu masu zuwa saboda rauni a cinyarshi.

Sagna me shekaru 27 ya raunata ne a karawar Arsenal da Chelsea a ranar uku ga watan Okotoba abinda kuma ya janyo bai shiga cikin tawagar Faransa don buga wasannin share fage.

A don haka ana saran ba zai shiga fafatawarsu da Birmingham a ranar Asabar da kuma Shakhtar Donetsk a ranar 19 ga watan Oktoba.

Ana saran Cesc Fabregas da Theo Walcott zasu koma fagen fama amma dai Robin van Persie da Thomas Vermaelen da Nicklas Bendtner duk zasu cigaba da jinya.