Cameron ya gayyaci shugaban Fifa Sepp Blatter

Blatter da Valcke
Image caption Shugaban Fifa Blatter da Sakatare Valcke

Shugaban FIFA Sepp Blatter zai hadu da Pirayi Ministan Birtaniya David Cameron a ranar Laraba don tattauna batun yinkurin Ingila na daukar bakuncin gasar cin kofin kwallon duniya a 2018.

Blatter da Sakatare Janar na FIFA Jerome Valcke zasu gana a ofishin pirayi ministan dake kan titin Downing kafin su hadu da magajin garin lardin London Boris Johnson.

Shugaban "England 2018" Geoff Thompson ya ce ganawar zata tabbatar da shirin samun karin bayanai akan yadda Ingila za ta kawo sauyi a wajen bunkasa gasar kwallon duniya.

Cameron ya gayyaci Blatter domin sharen fage kafin jami'an FIFA su kada kuri'a a ranar biyu ga watan Disamba akan kasar da za a baiwa damar daukar bakuncin gasar.

Ingila da Rasha da kuma hadin gwiwar Spain-Portugal sai kuma na Holland-Belgium ne ke fafatukar gannin an basu damar a 2018.