Kaptin din Zimbabwe Benjani Mwaruwari ya yi ritaya

Mwaruwari
Image caption Benjani Mwaruwari ya ce zai maida hankali a Balckburn

Kaptin din Zimbabwe Benjani Mwaruwari ya yi ritaya daga bugawa kasar kwallo bayan sun tashi babu ci tsakaninsu da Cape Verde a ranar Lahadi.

Ya shaidawa jaridar Herald cewar"na yanke shawara kuma ina ganin cewar sabbin jini zasu iya".

Dan shekaru talatin da biyu, Mwaruwari ya kulla yarjejeniya ta shekara guda da kungiyar Blackburn Rovers a watan Agusta kuma ya ce zai maida hankali akan taka leda a kungiyar.

Tsohon dan kwallon Manchester City din ya kasance kaptain din Warriors tun a shekara ta 2006 inda ya maye gurbin Peter Ndlovu.

Duk da cewar Mwaruwari ne dan kwallon da yafi kowanne shahara a Zimbabwe, amma dai yana fuskantar suka a wajen 'yan kasar saboda suna zargin baya taka musu leda kamar yadda yake yiwa kungiyarshi.