Uefa za ta bincike tashin hankali a wasan Serbiya da Italiya

Platini
Image caption Shugaban Uefa Michel Platini

Hukumar dake kula gasar kwallon Turai Uefa ta kaddamar da bincike akan tashin hankali tsakanin magoya bayan Serbia abinda ya janyo aka dakatar da wasa tsakaninsu da Italiya na sharen fage na gasar kasashen nahiyar Turai.

Tashin hankalin daya auku a Genoa dai ya janyo an samu jinkiri kafin a fara wasan sannan kuma minti shida da fara wasan sai aka dakatar.

Za ayi amfani da rahoton alkalan wasan wajen gudanar da binciken.

Wasu daga cikin hukuncin da Uefa zata iya dauka akan batun shine cin tara, ko kuma rufe filin wasan ko kuma daina yin duk wani wasa na gasa a cikin filin.

Abinda ya faru a filin Genoa din za a tattauna shi a taron Uefa na ranar 28 ga watan Oktoba kuma watakila a hukunta hukumar dake kula da gasar Italiya.