Kalusha Bwalya yaki yin murabus a Zambia

Bwalya
Image caption Shugaban kwallon Zambia Kalushi Bwalya

Shugaban hukumar dake kula da kwallon Zambia-FAZ Kalusha Bwalya yaki amincewa da kiraye kirayen cewar ya sauka daga kujerarshi.

Kiraye kirayen ya zamo ne bayan wasu manyan jami'an FAZ hudu suka yi murabus saboda nuna rashin jin dadinsu akan salon mulkin Bwalya.

A halin yanzu dai manya manyan klub klub na kasar Zambia sun bi sawun kiraye kirayen cewar Bwalya ya sauka daga mukaminshi.

Kalusha Bwalya ya bayyana cewar "an zabe mu saboda haka a barmu mu kamalla wa'adinmu a 2012".

Bwalya ya kara bayyana cewar hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta aike mashi da wasikar nuna goyon baya akan mulkinshi.