CAF za taci tarar kungiyar Esperance ta Tunisia

Caf
Image caption Kofin da klub klub na Afrika ke takara akai

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Afrika Caf ta ce za taci tarar kungiyar Esperance ta Tunisia saboda magoya bayanta sun kaiwa 'yan sanda hari kuma sun cire kujerun zama a filin wasa lokacin karawarsu da Al Ahly ta Masar.

Daraktan kwallon na Caf Abdel-Moneim Hussein ya ce hukumar za taci tarar Esperance kudade saboda rashin ladabin magoya bayanta.

Akalla 'yan sanda goma sha daya ne suka samu raunuka a yayinda aka kama 'yan Tunisia 14 bayan wasan a filin Alkahira inda Al Ahly ta doke Esperance daci biyu da daya a ranar uku ga watan Oktoba.

A ranar Lahadi mai zuwa ne za ayi bugu na biyu a birnin Tunis.

Masu lura da filin wasan sun bayyana cewar anyi barna data kai na dala dubu hamsin da biyu.