Rooney ya karyata Ferguson

Wayne Rooney
Image caption Wayne Rooney ya shiga cikin matsala a 'yan kwanakin nan

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney ya yi kalaman da suka sabawa na kociyansa Alex Ferguson, inda yace baiji rauni a idan sawunshi ba a kakar wasanni ta bana.

Ferguson ya cire Rooney a wasan da United ta tashi 2-2 a Bolton, sannan yaki sanya shi a wasansu da Valencia da kuma Sunderland, yana mai cewa dan wasan ba shi da lafiya.

Sai dai Rooney ya taka leda a wasan da Ingila ta buga da Montenegro ranar Talata.

"A'a, bani da wata matsala a idan sawuna," a cewar Rooney, lokacin da aka tambaye shi game da lafiyarsa.

Yayinda aka tambaye shi ko me yasa Alex Ferguson ya ce yana da rauni, sai yace: " Nima ban sani ba."

Rooney bai yi wani kokari a kakar wasanni ta bana - ya zira kwallo daya ne kawai ta bugun fanareti a wasanni biyar din da ya bugawa United.