Barcelona da Real Madrid sun haskaka a Spain

Ronaldo
Image caption Christiano Ronaldo ya ciwa Madrid kwallaye biyu a karshen mako

Andres Iniesta da Carlos Puyol sun ciwa Barcelona kwallaye a wasan data doke Valencia daci biyu da daya, amma duk da haka Real Madrid ce ta dare saman teburin gasar La Liga bayan ta casa Malaga daci hudu da daya.

Valencia ta shiga wasan a matsayin ta farko a gasar Spain sannan kuma babu kungiyar data samu nasara akanta kafin Barca ta casa ta.

Kungiyar Real Madrid karkashin jagorancin Jose Mourinho ta dare saman teburin gasar inda take da maki 17 a yayinda Barca ke ta biyu da maki 16.

Sakamakon wasannin mako na bakwai:

*Racing Santander 1 - 0 Almería *Deportivo La C… 0 - 0 Osasuna *Levante 2 - 1 Real Sociedad *Mallorca 0 - 1 Espanyol *Atlético Madrid 2 - 0 Getafe *Barcelona 2 - 1 Valencia *Málaga 1 - 4 Real Madrid