TP Mezembe ta kai wasan karshe na gasar zakarun Afrika

Mezembe
Image caption TP Mezembe ta kokarin kare kofin data lashe a bara

Kungiyar TP Mazembe ta jamhuriyar demokradiyyar Congo ta tsallake zuwa wasan karshe na gasar zakarun Afrika bayan ta tashi babu ci tsakaninta da JS Kabylie ta Aljeriya a ranar Asabar.

A bugun farko na zagayen kusada karshe dai TP Mezembe ta lallasa JS Kablylie daci uku da daya.

Mezembe wacce ta lashe kofin Afrika sau biyu a baya, nada damar kare kofinta bayan ta kai wasan karshe sau biyar a tarihi.

Mazembe ta lashe gasar a 1967 da 1968 sannan kuma aka doke ta a 1969 da 1970.

Kungiyar da jamhuriyar Congo za ta hadu da kungiyar data samu nasara a wasa tsakanin Esperance ta Tunisia da kuma Al Ahly ta Masar wadanda zasu kara a ranar Lahadi.