Andy Murray ya lashe gasar Shanghai Masters

Murray
Image caption Andy Murray ya lashe kofina biyu a bana

Andy Murray ya kara nuna cewar shi ba kanwan lasa bane a fagen Tennis a duniya bayan ya samu galaba akan Roger Federer a wasan karshe na gasar Shanghai Masters.

Murray din ya lashe gasar ce sakamakon doke Federer da seti biyu a jere.

Wannan nasarar ta kawo karshen matsalar da Murray ya samu inda aka fiddashi kafin yayi nisa a gasar US open kuma wannan ta zamo nasara ta biyu kenan daya samu a bana.

Wasan tsakanin Federer da Murray an kamallashi ne cikin awa daya da minti ashirin da biyar.