Ryan Giggs ya turgude kafadarshi

Giggs
Image caption Ryann Giggs ya dade yana murza leda

Dan kwallon Manchester United Ryan Giggs ya turgude kafadarshi abinda ya sanya zai shafe lokaci yana jinya.

Dan shekaru talatin da shida, Giggs mai dade da dawowa ba daga rauni inda ya shafe makwanni biyu yana jinya.

Jinyar da Giggs din zai yi zata iya kawo wa United cikas ganin cewar shine kadai dan kwallon da a yanzu yake taka leda ta hagu a klub din.

Kocin United Sir Alex Ferguson ya shaidawa MUTV cewar "rashin Ryan babbar rashine a wajenmu".

Ya kara da cewar "Ryan yaji rauni ne a wasanmu da Bolton, kuma dama ciwon ya kwana biyu a jikinshi".