CAF:Esperance za ta hadu da TP Mezembe a wasan karshe

Mezembe
Image caption Tawagar 'yan kwallon TP Mezembe

Kungiyar Esperance ta Tunisia za ta hadu da TP Mazembe ta Jamhuriyar demokradiyar Congo a wasan karshe na gasar zakarun Afrika a wata mai zuwa.

Esperance din ta doke Al Ahly a bugu na biyu na wasan kusada karshe daci daya me ban haushi inda dan Najeriya Micheal Eneramo yaci kwallon.

Ita kuwa kungiyar TP Mazembe ta samu nata gurbin ne bayan ta samu galaba akan JS Kabylie ta Aljeriya.

Mezembe wacce ta lashe kofin Afrika sau biyu a baya, nada damar kare kofinta bayan ta kai wasan karshe sau biyar a tarihi.

Mazembe ta lashe gasar a 1967 da 1968 sannan kuma aka doke ta a 1969 da 1970.

Za a buga wasan karshen ne a karshen makon 12-14 ga watan Nuwamba.

Duk kungiyar data lashe gasar za a bata kyautar dalam Amurka miliyan daya da rabi kuma kungiyar ce zata wakilci Afrika a gasar cin kofin klub klub na duniya a watan Disamba a Haddadiyar daular Larabawa.