Watakila Rooney ya bar Manchester United a badi

Wayne Rooney
Image caption Wayne Rooney na zaune a benci a wasan United da West Brom

Rahotanni na nuna cewa akwai yiwuwar Wayne Rooney ba zai kulla sabuwar yarjejeniya da Manchester United ba.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya rawaito cewa tuni aka shaida wa kulob din na Manchester United matsayin da dan wasan ya dauka.

Yarjejeniyar dan wasan mai shekaru 24, za ta kare ne a karshen kakar wasanni ta 2012, kuma bayanai sun nuna cewa tattaunawa domin sabuntawa tsakaninsa da United din ta wargatse.

An yi ta rudanin cewa za a sayar da Rooney a watan Janairu, inda aka ce Real Madrid ta nuna sha'awar sayensa.

Sai dai United ta karyata zancen.

Dangantaka tsakanin Rooney da kociyansa Alex Ferguson ta yi tsami a 'yan makwannin da suka wuce.

Dan wasan bai buga wasan da United ta kara da Everton a watan da ya wuce ba, bayan wani zargin da aka yi kan abubuwan da suka shafi rayuwarsa ta sirri.

Har ila yau Ferguson ya ajiye shi a sauran wasannin da suka biyo baya, yana mai cewa yana fama da rauni.

Sai dai ledar da dan wasan ya taka a wasan da Ingila ta yi da Montenegro ranar Talatar da ta wuce, ya sa shakku kan kalaman na Fergoson.

Baya ga Real Madrid, akwai kungiyoyi da dama da ake tunanin suna neman dan wasan, wadanda suka hada da Manchester City da Chelsea da Barcelona.