Kocin Middlesbrough Gordon Strachan ya yi murabus

Strachan
Image caption Gordon Strachan ya jagoranci Middlesborough na shekara guda

Kocin Middlesbrough Gordon Strachan ya bar kungiyar bayan shafe kasada shekara guda a kungiyar.

A karshen mako ne Leeds United ta doke Middlesbrough daci biyu da daya, abinda kuma ya sanya suka koma na ashirin akan teburin gasar Championship.

Strachan ya samu nasara ne a karawa 13 cikin wasanni 46 a matsayin mai horadda 'yan kwallon inda ya maye gurbin Gareth Southgate a watan Oktoban 2009.

Kawo yanzu dai kungiyar bata sanarda wanda zai jagoranci 'yan kwallonta a wasansu na ranar Talata tsakaninsu da Nottingham Forest .