Al Ahly ta kai karar alkalin wasa wajen Caf

Fadi
Image caption Dan kwallon Al Ahly Mohammed Fadi

Kungiyar Al Ahly ta Masar ta kai karar alkalin wasan da ya jagoranci wasanta da Esperance ta Tunisia zuwa hukumar dake kula da kwallon kafa a Afrika-Caf.

Dan Ghana Joseph Lamptey ne ya hura usur a karawar da akayi tsakanin kungiyoyin biyu a Tunis.

A cewar Al Ahly da hannu Mike Eneramo ya ci kwallon daya baiwa Esperance nasara a fafatawar, amma sai alkalin wasa yaki daukar hukunci.

Wata sanarwa daga adreshin yanar gizon Ahly ta bayyana cewar alkalin wasan 'ya nuna san kai'.

Da aka sake duba yadda Eneramo yaci kwallon a talabijin, ya bayyana kuru kuru cewar ya gyara kwallon da hannu kafin ya shigar da ita raga.

Kocin Al Ahly Hossam al-Badri ya yi zargin cewar Lamptey ya jawo musu kafar angulu a yinkurinsu na samun kyautar dala miliyan daya da rabi da kuma damar buga gasar cin kofin klub klub na duniya a karshen bana.

Esperance a halin yanzu zata kara da TP Mazembe ta Congo a wasan karshe a wata mai zuwa.