An ci tarar Cagliari saboda zagin Samuel Etoo

Etoo
Image caption Magoya baya a Italiya sun yi mashi ihun kin jini

An ci tarar kungiyar Cagliari ta Italiya Euro dubu ashirin da biyar saboda magoya bayanta sun yiwa dan kwallon Inter Milan dan Kamaru Samuel Eto'o ihu na wariyar launin fata a wasansu na ranar Lahadi.

Hukumar dake kula da kwallon Italiya ce ta yanke wannan tarar da kungiyar za ta biya.

Alkalin wasa Paolo Tagliavento ya dakatar da wasan na minti uku bayan da aka yita nuna kin jinin Eto'o a filin wasan.

Nan take kuma aka bada sanarwa a cikin filin wasan cewar idan ba'a daina zagin Eto'o ba , tabbas za a dakatar da wasan.

Bayan an tashi wasan inda Eto'o din ya ciwa Inter Milan kwallon daya bata nasara a karawar sai kocin Cagliari Pierpaolo Bisoli yace an yi mummunar fahimta ne akan ihun.