Chelsea ta tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar zakarun Turai

Anelka
Image caption Anelka ne ya zira kwallo na biyu a ragar Spartak

Chelsea ta tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar zakarun turai bayan ta samu galaba akan Spartak Moscow daci biyu da nema a wasan da suka buga a ciwar roba a Moscow.

Dan Rasha Yuri Zhirkov ne yaci kwallon farko a minti na ashirin da uku sannan Nicholas Anelka shi kuma ya ci na biyu kafin a tafi rabin lokaci.

Chelsea ta buga wasanne banda Didier Drogba da Frank Lampard kuma wasan shine na dari da Carlo Ancelotti ya jagoranta a gasar zakarun Turai.

Bayan karawa uku, a yanzu Chelsea nada maki tara a yayinda Spartak Moscow take ta biyu da maki shida.