Masar ta rikito daga jerin manyan kasashe a fagen kwallo

Masar
Image caption 'Yan kwallon Masar ta murnar lashe gasar kofin Afrika a 2010

Zakaran kwallon Afrika wato Masar ta fita daga cikin jerin manyan kasashe goma a fagen kwallon kafa, kamar Fifa ta bayyana jerin a ranar Laraba.

Tawagar 'Pharaohs' ta koma na goma sha daya abinda kuma ke nufin cewar babu wata kasa a nahiyar Afrika dake cikin jerin manyan kasashen kwallo a duniya.

Ghana ta hau sama inda ta koma ta 17 a yayinda Ivory Coast take ta 19.

Zakaran kwallon duniya Spain har yanzu itace a saman jerin na Fifa sai Netherlands ta biyu a yayinda Brazil take ta uku.

Nijer saboda kashin data baiwa Masar ta zama ta 26 a Afrika sannan ta 100 a duniya.

Jerin a Afrika:

1. Masar (11 a duniya)

2. Ghana (17a duniya)

3. Ivory Coast (19 a duniya)

4. Aljeriya (33 a duniya)

5. Najeriya (34 a duniya)

6. Burkina Faso (37 a duniya)

7. Kamaru (38 a duniya)

8. Gabon (39 a duniya)

9. Tunisia (45 a duniya)

10. Guinea (47 a duniya)