Fifa ta dakatar da Amos Adamu da Reynald Temarii

Amos da reynald
Image caption Jamian Fifa da aka dakatar Amos Adamu da Reynald Temarii

Hukumar dake kula da gasar kwallon kafa a duniya Fifa ta dakatar da jami'anta biyu na wucin gadi wato Amos Adamu na Najeriya da Reynald Temarii na Tahiti saboda zargin cin hanci da rashawa.

Ana zargin jamian biyu ne da yinkurin sayar da kuri'ar su ta zabar kasar da zata karbi bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarar ta 2018.

Kwamitin da'a na Fifa da gaggarumin rinjaye ya amince da dakatarwar amma dai mutane biyun sun musanta zargin.

Jaridar Sunday Times, ce ta wallafa cewar Mr Amos Adamu da kuma Reynold Temarii dan Kasar Tahiti, dukkaninsu sun nuna a shirye su ke su sayar da kuri'ar su ta zabar kasar da zata karbi bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarar ta 2018 da kuma na 2022.

Jaridar ta ce, Mr Adamu ya bukaci a bashi dala dubu dari takwas don ya gina filayen wasa a Najeriya, da aka tambaye shi yana gani idan a ka bashi kudi don gudanar da aikin kashin kansa hakan za ta sa ya sauya yadda zai kada kuri'a, sai ya ce, ''lallai hakan zai yi tasiri.Tabbas kuwa''.